HomeSashen HausaAn Janye sojoji kusan awa guda kafin harin Maga – Gwamna Idris

An Janye sojoji kusan awa guda kafin harin Maga – Gwamna Idris

-

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris, ya bayyana damuwa kan janyewar jami’an soji daga makarantar sakandire ta Maga, jim kaɗan kafin ƴanbindiga su sace ɗalibai da dama.

Idris ya yi wannan bayani ne a yau Juma’a a Birnin Kebbi, yayin da yake karɓar bakuncin shugaban ƙungiyar kwadago na ƙasa NLC Joe Ajaero, wanda ya ziyarci jihar don jajanta masa bisa harin.

Ya ce lamarin abin takaici ne kuma mai tayar masa da hankali, musamman ganin cewa tun da fari, gwamnatin jihar ta samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar kai hari kuma nan da nan ta kira zaman gaggawa na tsaro don daukar mataki.

A cewarsa: “A matsayinmu na gwamnati mai saurin daukar mataki, mu na samun bayanan sirri kan yiwuwar harin, sai muka kira ganawar tsaro. A yayin ganawar, jami’an tsaro sun tabbatar mana da cewa babu komai kuma za su kai jami’an su wajen.

Sai aka kai sojoji zuwa makarantar amma zuwa karfe 3 na dare aka kwashe su. Karfe 3:45 na dare aka kai harin, kamar yadda NAN ta ruwaito Gwamnan ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gov Radda seeks forgiveness from Katsina residents as APC launches Tinubu/Dikko 2027 campaign council

Katsina State Governor Dikko Umaru Radda, has appealed to residents of the state to forgive him for any offence he might have committed against them...

Nigerian customs service inaugurate 2026 cadet officers at Lagos training college

By Abdulmumini Ashiru The Nigeria Customs Service (NCS) on Thursday inaugurated its 2026 Cadet Officers at the Customs Training College, Ikeja, Lagos, marking the formal start...

Most Popular